Sabuwar doka yaki da ta'addanci a Masar

Hakkin mallakar hoto
Image caption 'Yan adawa na ganin shugaba Al-sisi na shirin muzguna musu

Shugaban kasar Masar Abdel Fattah al-Sisi, ya amince da wasu tsauraran matakai na yaki da ta'addanci domin karfafa yunkurin kasar na magance barazanar da masu ta da kayar baya ke yi.

Daga yanzu duk wanda aka samu da laifin kafawa ko jagorantar kungiyar da ke da alaka da ta'addanci, zai fuskanci hukunci kisa ne ko kuma daurin rai da rai a gidan yari.

Haka kuma za a gaggauta shari'ar duk wasu da ake zargi da tayar da kayar baya.

Kazalika, duk wani dan jarida daya ba da rahotanni da suka saba adadin da hukumomi suka fitar a duk wani harin da aka kai, za a ci tarar sa a kalla dala dubu ashirin da biyar.

Sai dai masu fafutika sun ce za a rika amfani da dokar wajen kuntatawa 'yan adawa tare da takaita 'yancin fadin albarkacin baki.