Sabon rikici ya barke a arewacin Mali

Image caption Mayakan azbinawa na nema kasar kansu

Mutane da dama ne suka hallaka a wata arangama tsakanin Abzinawa 'yan aware da mayaka masu goyon bayan gwamnati a arewacin kasar Mali.

Jagororin soji daga babbar kungiyar Abzniawa 'yan tawayen na cikin wadanda aka bayyana sun mutu.

Duka bangarorin na zargin junansu da fara fadan kusa da arewacin garin Kidal.

A cikin watan Yuni ne, gwamnatin kasar Mali ta rattaba hannu da Abzinawa, tare da yi musu tayin 'yancin cin gashin kai.

Hare-haren kungiyoyi masu kaifin kishin Islama sun yi mummunan tasiri kan arewacin kasar Malin.