Sojin Nigeria sun yi wa Shekau raddi

Hakkin mallakar hoto AP

Rundunar sojin Najeriya ta ce za ta murkushe kungiyar Boko Haram ko da Shekau ya na raye ko kuwa a mace.

Rundunar ta bayyana haka ne bayan wani faifan murya da aka fitar aka ce na Abubakar Shekau, shugaban kungiyar Boko Haram ne inda ya musanta cewar an maye gurbinsa, kuma ya ce yana nan a raye.

Kakakin rundunar sojin kasa ta Najeriya, Sani Usman Kukasheka ya bayyanawa BBC cewar "Mu ba mu damu ba ko shugaban kungiyar Boko Haram yana nan a raye ko a mace, mu dai muhimmin abin da mu ka saka a gaba shi ne na tabbatar da cewar mun murkushe kungiyar Boko Haram nan da watanni uku kamar yadda shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya umarce mu".

A karon farko kuma Jagoran ya ambaci kansa a matsayin Gwamnan daular musulunci na Afrika ta yamma mai munaya'a ga kungiyar IS.

Ya kuma kalubalanci Shugaban kasar Chadi da kuma Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari kan umarnin da ya bayar na murkushe su cikin watanni uku.

A baya dai an yi ta rade radin cewar Shekau ya mutu.

A makon da ya gabata ma shugaban Chadi Idriss Derby ya ce an maye gurbinsa.

A makon da ya gabata ne Shugaba Buhari ya umarci dakarun sojin Najeriya su murkushe kungiyar Boko Haram cikin wantanni uku.