An soma taron sulhu kan Sudan ta Kudu

Image caption Ana taron sulhunta kungiyoyin Sudan ta Kudu a kasar Habasha.

Ana zantawa tsakanin kungiyoyi a Sudan ta Kudu domin samun daidaito na zaman lafiya kafin wa'adin yarjejeniyar ta kawo karshe a yau Litinin.

Akwai yiwuwar a sanyawa kasar takunkumi daga kasashen waje idan bangarorin da ba sa jituwa suka gaza samun matsaya.

Duk kungiyoyin biyu sun bukaci a kara masu lokaci domin su warware matsalolin da suka hada da tsarin mika mulkin kasar.

Masu sulhunta su a yankunan, wadanda suka hada da Shugaban kasar Kenya da na Uganda, suna taro a Addis Ababa babban birnin kasar Hababasha, inda Firayi ministan kasar ma yake cikin taron.

A baya dai ba a yi nasara a duk wani yunkurin a sulhunta su ba.