Wane wata hadarin jirgin sama ya fi muni ?

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Watan Agustan shekara 1985, shi ne watan da hadarin jirgi ya fi kowanne muni.

A watan Agustan shekarar 1985, an samu karin mace-mace sakamakon hadarin jiragen sama, fiye da duk sauran watanni.

Me ye dalilin da yasa abin ya kazanta haka?

Akwai matsaloli da yawa a tarihin sifirin jiragen sama, amma akwai guda daya da ya fi shahara.

Shekaru talatin da suka wuce, fasinjojin jirgi su 720 suka rasa rayukan su a cikin wata daya, fiye da duk sauran watanni.

Mutane sun hallaka a hadura hudu a lokuta daban-daban a watan Agustan shekarar 1985, kuma kowanne hadari da nasa dalilin daban da janyo shi.

Jiragen sun hada da samfarin 747 har ma da kananan masu tagwayen injuna wadanda ba su wuci daukan mutane takwas ba.

Akwai jirgin Japan mai suna 'Japan Air flight 123', wanda hadarin sa ya fi kowanne muni, inda mutane 520 suka rasu cikin su 524.

An samu karin mutuwar mutane 137 lokacin da jirgin 'Delta flight 191' ya yi hatsari sakamakon iska mai karfi a lokacin da ya doshi sararin samaniyar filin saukar jirgin sama na Dallas-Fort Worth International.

Wata gobara da aka samu cikin jirgin 'British Airtours flight 28M' a filin jirgin Manchester Airport, ta janyo mutuwar mutane 55.

Cikin jiragen, wanda ya fi su kankanta shi ne 'Bar Harbor Airlines flight 1808', kuma duk an yi hasarar rayukan wadanda suke ciki lokacin da ya yi hatsari cikin filin jirgin garin Maine da ke Amurka.

'Wasiyya'

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kowane jirgi na dauke da irin wasiyyar da ya bari, wurin alhinin wadanda suka rasu.

Kowane jirgi na dauke da irin na shi wasiyyar da ya bari, wurin alhinin wadanda suka rasu da kuma canji a ilimin fasaha da aka karu da shi sakamakon haduran da aka yi.

A ranar 12 ga watan Agustan shekarar 1985, hatsarin jirgin da ya fi muni, shi ne wanda ya auku na jirgin 'Japan Air Lines Flight 123-kirar Boeing 747', wanda ya taso daga Tokyo a hanyarsa zuwa Osaka , sakamakon budewar abin da ke toshe iskar jirgin.

Hakan ya janyo fashewar jelar jirgin, inda na'urar da ke aiki da karfin ruwa na jirgin ya lalace, hakan kuma ya sa jirgin ya fara girgiza.

Farfesa Graham Braithwaite, wani mai sharhi kan bincike a kan amincin ababan hawa da hadura a jami'ar Cranfield, ya ce "Masu tuka jirgin sun nuna jaruntaka sama da sa'a daya, amma da jirgin ya kara yin kasa, sai suka bayar da rahoton cewar basa su iya tsayar da ita ba".

An samu mintuna 32 bayan fashewar iskar jirgin, hakan kuma ya bai wa fasinjojin damar tura sakonnin ban kwana ga 'yanuwan su.

Masu bincike sun bayyana cewa an samu hatsarin ne sakamakon gyaran da aka yi wa jirgin maras inganci, lokacin da jelar jirgin ta karce kasan filin jirgi, shekaru bakwai da suka wuce.

'Ba sabon ba'

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Yuri Andropov ta gayyaci 'yar makarantar Amurka Samantha Smith zuwa kasar Rasha a shekarar 1983.

Ba a saba samun irin wannan bala'i na hadarin jirgi sakamakon rashin inganci a gyara ba, inda aka daura nauyin laifin a kan masu gyaran da masu kula da jiragen.

John Beardmore, yana cikin wadanda suka rayu a hadarin jirgin 'British Airtours flight 28M' inda jirgin ya kama da wuta a filin tashin jirgin ranar 22 ga watan Agustan, shekara 1985 aka kuma yi hasarar rayuka 55.

Har yanzu yana tunawa da yadda ya yi kokarin neman mafita daga cikin jirgin.

Hakkin mallakar hoto Getty

Hadarin karshe da ya auku a shekarar 1985, shi ne lokacin da jirgin 'Bar Harbor Airlines 1808' da ya auku kadan da ya iso filin jirgin Auburn/Lewiston Municpal na Maine a Amurka, inda dukkan fasinjojin da matukan jirgin suka rasu.

Tun shekarun da suka gabata bayan shekarar 1990, an samu sauki a haduran jiragen sama, duk da an samu kari a shekara ta 2014.

Inda aka samu bala'i na haduran jirage da suka hada da jiragen Malaysia Airlilines biyu--- mai kirar MH370 ya bace, shi kuwa dayan mai kirar MH17 aka harbo shi har kasa a sararin samaniyar kasar Ukraine.

Akwai kuma jirgin 'Air Asia' wanda ya bace a hanyar sa na zuwa Singapore.

Haduran da aka samu a watan Agustan shekarar 1985, ya janyo sauyi wurin inganta amincin jirage.