Mutane 60 sun hallaka a kauyen Yobe

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Rikicin Boko Haram ya raba miliyoyin mutane da muhallansu

Mutane a kalla 60 sun rasu ta hanyar kodai nutsewa a ruwa, ko harbin bindiga a lokacin da suke kokarin gujewa harin 'yan Boko Haram a jihar Yobe da ke arewacin Nigeria.

Lamarin ya faru ne a ranar Alhamis da ta wuce amma sai yanzu ake samun bayanai kan batun.

Shaidu sun bayyana cewar mayakan Boko Haram a kan babura da motoci sun je kauyen Yadin Kukawa da ke jihar Yobe inda suka yi ta harbin kan mai tsautsayi a daidai lokacin da ake ruwan kamar da bakin kwarya.

Mutanen kauyen wadanda a lokacin suna shirin Sallar Magariba ne sai suka firgice suka tsere a yayin da wasu suka fada cikin rafi suka nutse saboda ba su iya ruwa ba.

Wani da ya tsira ya ce washe gari sun kirga gawawwakin yara kanana 60 a kan tituna.

Wasu rahotannin sun ce mutane kusan 150 ne suka rasu saboda har yanzu wasu iyayen ba su ga 'ya'yansu ba.

Ana kallon harin a matsayin na daukar fansa ne saboda a makon da ya gabata wasu maharba sun hallaka 'yan Boko Haram a kauyen.

'Yan Boko Haram sun hallaka daruruwan mutane a Nigeria tun lokacin da shugaba Buhari ya hau karagar mulki.

Shugaban kasar ya umurci dakarun Nigeria su murkushe Boko Haram a cikin watanni uku masu zuwa.