Tasirin dokar hana kantuna zubar da abinci a Faransa

Hakkin mallakar hoto Reuters

Wani shiri na samar da doka irin ta Faransa na hana manyan kantuna lalata ragowar kayan abinci da basu sayar ba, kuma ya ke basu kwarin gwiwar su bayar sadaka yana dagawa masu kantuna hankali, wadanda su ka ce suna kokari wajen rage barnar ragowar kayan abinci.

A tsarin dokar, shaguna wadanda girmansu ya kai murabba'in mita 400 dole su saka hannu a kwantiragi da gidajen da su ke taimakawa masu sadakar abinci da bankunan abinci kuma su fara ba su ragowar kayan da ba a sayar ba.

Wannan tsari ya biyo bayan wani kamfe da mai ra'ayin rikau na Arash Derambarsh ya jagoranta, wanda ya ce ya yi matukar jin takaicin irin halin da ya ga marasa galihu a hunturun bara inda ya ga suna ta bincikar kwandunan sharan manyan katuna.

Derambarsh, kansila na wajen garin Courbevoie, ya fara kamfe din sa ne ta hanyar karbar ragowar abincin da ba a sayar ba kuma yana baiwa mabukata.

Daga nan sai ya kaddamar da wani shafi na korafi a intanet wanda ya karawa sabuwar dokar kaimi.

Duk da cewar gidajen kula da mabukatu sun yi na'am da wannan doka, suna tsoro kar abinci ya yi musu yawa kuma su rasa yadda za su yi da shi.

Shugaban gidan cin abinci na mabukata na Restos du Coeur Olivier Berthe ya ce "ba za mu bari a tirsasa mana mu karbi taimakon da ba mu bukata ba. Ba za mu zama wurin zubar da shara ba."

Hakkin mallakar hoto Reuters

Jacques Bailet, shugaban bankin ajiyar abinci na kasar shi ma ya ce, akwai yiwuwar gidajen abinci ba za su iya jurewa ba.

"Bankinmu zai bukaci karin ma'aikata da karin manyan motoci da dakunan masu sanyi na ajiyar kayan abinci. Amma kuma sai da kudi za mu iya samun duk wadannan abubuwa - kuma kudade sunyi wahala a 'yan kwanakin nan, in ji Bailet.

Manajan babban kantin Leclerc da ke Templeuve wanda ke kusa da Lille, Thomas Pocher ya ce daga cikin mutane bakwai da suka shiga shagon, ya riga ya baiwa mabukacin abinci daya sadaka.

Kantin na samar da tan 250 na abinci, da ba a bukata a duk shekara kuma ya na da kwantragi da gidajen taimakawa mabukata na kasar.

Sai dai kuma harajin da ake sakawa kayan abincin ya na taimakawa masu kantuna wajen mayar da kudaden da suka yi hasara.

Ya ce "A nan Templeuve mun saka hannu a kwantragi da manoma na yankin da su rika yin miya da kayan lambu da suka fara yaushi. Wannan abu ne da a da bamu sayarwa kuma yanzu muna da kwararen mai girki wanda ya ke tsara yadda za a yi miyan kuma mutane suna matukar son shi".

" Maganar zubar da abinci tana da muhimmanci, amma bai kamata a bar maganar a hannun masu gwagwar mayar kula da alkitan muhalli da mutane wadanda su ke so su kawo sauyi a al'uma. Za mu iya yi da kanmu a matsayinmu na masu kasuwanci," in ji Pocher

Derambarsh yana da wasu daban wadanda suma suke sukan shi.

Wasu 'yan majalisa masu ra'ayin gurguzu sun adawa da shi saboda jawo hankulan da yayi na mutane da dama a kan lamarin a intanet, a yayinda su suka shafe shekaru suna aiki a kan maganar.

Hakkin mallakar hoto Reuters

Wasu sun ce a cikin sama da tan miliyan bakwai na abincin da ake zubarwa a Faransa,a cewer ma'aikatar da ke kula da alkita muhalli na Faransa, mutane da kansu su ke zubar da kashi 67 cikin 100.

Kuma gidajen sayar da abinci suna zubar da kashi 15 cikin 100, yayinda kantuna da masu rabon kayayyaki suna zubar da kashi 11 cikin dari da duka.

Derambarsh, wanda da ne ga 'yan gudun hijirah daga Iran, an haife shi ne a birnin Paris a shekarar 1979, kuma ya yi shekaru hudu a Iran yana yaro, ya yi watsi da sukar da ake yi masa inda ya ce ra'ayoyinsa masu saukin ganewa ne.

"A lokacin da na ke yaro na yanke shawarar idan na girma zan yi wani abu da zai taimakwa al'uma," in ji Derambarsh.

Ya dan samu koma baya na dan lokaci, kwamitin kundun tsarin mulkin kasar Faransa wanda ke nazari game da sabbin dokoki domin tantance dacewarsu ya yi fatali da dokar bisa sabarwata da ka'idoji.

Yanzu dole a sake nazari kan kudirin dokan wanda ka iya daukan wani dogon lokaci.

A yanzu, magoya bayan korafin sun kai sama da 630,000. Idan har ya kai miliyan day, dole a duba yuwuwar shirin - duk da dai zata iya kin yanke hukunci.