Layukan mai sun dawo a Kano

layin mai Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Dillalan fetur din sun ce ba za su iya sayar da man a farashin gwammnati na Naira 87 lita ba saboda wahalhalun dakonsa daga Legas

A jihar Kano dai ana fama da karancin man fetur musamman a gidajen mai na 'yan kasuwa masu zaman kan su.

Wakilin BBC da ya zaga birnin yace a gidajen mai kalilan ne ake samun man inda ababen hawa suka yi cincirindo domin sha.

Shugaban kungiyar dillalan man fetur mai zaman kansu a jihar yace suna sayen man da tsada, ba kuma za su iya sayar da shi a farashin da gwamnati na naira 87 lita ba.

Dillalan man sun ce hakan ba zai yiwu ba in ba matatar man fetur din Kaduna ba ta soma aiki ba, aka kuma soma daukar man daga can.

Gwammnatin kasar dai ta soma farfado da matatun man fetur din kasar a inda matar man ta Fatakwal ya soma aiki. Ana sa ran matatan mai ta Kaduna iat ma za ta soma aiki gadan-gadan nan ba da dadewa ba.