Hajj: Maniyyatan Filato sun shiga rudani

mahajjata a Ka`aba Hakkin mallakar hoto

Yayin da ake shirin soma jigilar maniyyata aikin Hajji na Nijeriya zuwa kasar Saudiyya a wannan mako, wani rudani da aka shiga a hukumar Kula da jin Dadin Mahajjata ta Jihar Filato, ya rutsa da wasu maniyyata fiye da dari hudu, wananda ga alama ba za su samu sauke faralin a bana ba.

Sabbin shuwagabannin hukumar Kula da jin dadin Mahajjatan ne dai suka bayyana cewa ba su ga kudaden mutanen a asusu ba, bayan da suka karbi ragamar hukumar a watan jiya daga shuwagabannin da suka gabata, amma tsoffin shuwagabannin na cewa kudaden da suka karba daga maniyyatan tun a bara, sun yi mafani da su ne wajen gudanar da wasu ayyuka a hukumar.

Bayanai dai na cewa maniyyata aikin Hajjin fiye da dari hudu daga jihar Filato, sun biya kudin kujerarsu tun a bara, kama daga Naira dubu dari shida zuwa naira dubu dari bakwai kowannensu, da nufin zasu tafi aikin a bara, amma lamarin ya faskara, hukumomi kuma suka yi masu alkawarin cewa a bana zasu kasance farkon dauka, sai dai a banan ma yanzu basa cikin wadanda zasu tafi kasar ta Saudiyya domin sauke faralin sabo da tangarda da aka samu daga hukumar alhazai.

Matsalar dai ta kara dagulewa ne bayan sauya shugabancin hukumar Kula da Jin Dadin Mahajja ta jihar, sakamakon sauyin gwamnati da aka samu a bana, inda sabbin shuwagabannin suka bayyana cewa basu tarar da kudaden mahajjan da tsofofin jami’an hukumar suka karba a bara ba a cikin asusu ba.

Shugaban kula da aikin Hajji na bana a jihar ta Filato, Injiniya Danlami Abdullahi Muhammad, ya shaida wa BBC cewa sun kafa kwamiti domin bincika lamarin, amma dai daga cikin maniyyata dari hudu da talatin da wani abu, an iya kalato kujeru talatin aka bai wa wasunsu, sai dai kimanin dari hudun kam sai dai su yi hakuri.

Sai dai tsohon sakataren hukumar Kula da Mahajja ta Jihar Filato na baya-baya, Alhaji Salisu Musa, y a ce su ma tun 2012 suka gaji matsalar, sukan kuma yi amfani da kudaden wasu maniyyata wajen dawainiyar hukumar, kana a jinkirta zuwan maniyyatan sai shekara ta kewayo, sabo da karancin kudaden da gwamnatin da ta gabata kan bai wa hukumar alhazan.

Aikin Hajji dai na daya daga cikin shika-shikan addinin Islama guda biyar, da kowace shekara muliyoyin musulmi daga sassa daban-daban kan hallara kasar Saudiyya domin aiwatarwa, kuma dubban ‘yan Nijeriya ake sa ran zasu sauke faralin daga Nijeriya.