'Yan adawar Niger sun hade wuri guda

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Manyan adawar Nijar, Hama Amadou, Seyni Oumarou da kuma Mahamane Ousmane.

Wasu daga cikin manyan 'yan adawa a Niger sun hade wuri guda domin kalubalantar shugaba Issoufou a zaben shekara mai zuwa.

'Yan adawar daga jam'iyyu 30 da kungiyoyi farar hula da kuma na kwadago sun ce bukatarsu ita ce kwace mulki daga hannu jam'iyyar PNDS tarayya.

Manyan 'yan adawar sun hada da tsohon shugaban majalisar dokoki, Hama Amadou da kuma tsohon Firai minista, Seyni Oumarou da kuma tsohon shugaban kasa, Mahamane Ousmane.

Wata sanarwa da suka fitar ta ce "Mun yake shawarar kalubalantar Shugaba Mahamadou Issoufou domin hana shi samun mulki a karo na biyu."

A ranar 21 ga watan Fabarairun 2016 ne ake saran gudanar da zaben shugaban kasa a Nijar.

A bisa tsari dai, ana saran mutane miliyan bakwai da rabi ne za su jefa kuri'a a cikin al'ummar kasar su miliyan 17.