'Ba mu karbi makuden kudade ba'

Majalisar dokokin Nigeria Hakkin mallakar hoto national assembly
Image caption Majalisar dokokin Nigeria

Wasu 'yan majalisar dokoki a Najeriya sun musanta rahotannin da ke cewa daukacin 'yan majalisar dattawa da ta wakilai sun kashe fiye da Naira biliyan goma sha biyu cikin watanni uku da fara aiki a majalisar.

'Yan majalisun sun kuma ce ya zuwa yanzu sun shafe watanni uku ba tare da karbar albashi ba.

Kazalika 'yan majalisun sun ce sakamakon yanayin matsin tattalin arziki da kasar ke ciki, sun fara daukar matakai na ganin sun rage yawan albashin da kowane dan majalisa ke karba.

Alhassan Ado Doguwa mai tsawatarwa a majalisar wakilan Najeriya, ya shaida wa BBC cewa zarge-zargen da wasu ke yi cewa 'yan majalisun kasar sun karbi makuden kudaden ba gaskiya ba ne.