Sudan ta kudu na fuskantar takunkumi

Image caption An dade ana bata kashi tsakanin sojoji masu biyayya ga shugaban Sudan ta kudu ta na 'yan tawaye

Shugaban kasar Sudan ta Kudu, Salva Kiir, da babban abokin hamayyarsa Riek Machar, na fuskantar takunkumi daga kasashen duniya, bayan da suka gaza cimma yarjejeniyar tabbatar da zaman lafiya tsakanin su kafin cikar wa'adin da aka dibar musu.

Shi dai jagoran 'yan tawayen Riek Machar ya rattaba hannu a kan shawarwarin zaman lafiya da aka gabatar a tattaunawar da suka yi a kasar Habasha.

Wani mai shiga tsakani a tattaunawar ya ce gwamnatin Sudan ta Kudu na son yi nazarin amma kuma za ta rattaba hannun nan da kwanaki 15.

Kakakin fadar gwamnatin Amurka, John Kirby, ya ce gwamnatin ta Amurka ta yi takaicin yadda gwamnatin Sudan ta Kudu ta yanke shawarar kin sanya hannu a kan yarjejeniyar.

Ya kuma bukaci gwamnatin Sudan ta Kudu da ta sanya hannu cikin makwanni biyu da take da shi domin yin nazari.