Jirgin sama mara matuki mai nutso a ruwa

Jirgi mara matuki Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jirgin zai rika taimaka wa masu linkaya gano wurin da kifaye ke taruwa a cikin teku.

An fara kera wani dan karamin jirgi mara matuki da zai rika taimaka wa masu linkaya gano wurin da kifaye ke taruwa a cikin teku.

Jirgin na Fathom wanda ake sarrafawa da wayar salula na tafi da gidanka za a sanya masa na'urar daukar hoto kuma zai rika nutso cikin ruwa ya kuma ta so sama.

An kiyasta cewa kudin jirgin zai kai dala dari hudu da arba'in da biyar kuma wannan ne karon farko da aka kera don sayarwa jama'a irin wannan jirgi da ke shiga cikin ruwa.

Mutanen da suka kirkiro jirgin sun hada da Danny Vessels da abokan sa Matt Gira da Matt Webb da kuma John Boss kuma sun shafe watanni hudu ne suna aikin kera jirgin na Fathom.