Nigeria na binciken baiwa dan IS 'visa'

Image caption Kasashe da dama na neman Sheikh Ahmad al-Assir ruwa ajallo

Ma'aikatar harkokin wajen Nigeria ta ce ta kaddamar da bincike kan yadda aka yi wani fitaccen jagoran kungiyar IS ya samu takardar iznin shiga kasar watau visa.

Hukumomin Lebanon ne dai suka kama Sheikh Ahmad al-Assir wanda gwamnatocin kasashen da dama ke nema ruwa ajallo.

An damke Al'asir ne sa'adda yake kokari tashi daga birnin Beirut zuwa Nigeria dauke da fasfo din Falasdinu na jabu amma da sahihiyar takardar iznin shiga Nigeria watau visa.

Babban sakataren a ma'aikatar harkokin wajen Nigeria, Mr. Bulus Lolo ya shaidawa BBC cewa, mutumin wanda kwamanda ne a kungiyar IS a ba shi takardar izinin shiga Nigeria ne daga ofishin huddar jakadancin kasar da ke kasar Lebanon.