Ba a kai hari a Yobe ba — Sojin Nigeria

Dakarun sojin Nigeria Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Dakarun sojin Nigeria

Rundunar sojin Najeriya ta musanta cewa an kai hari tare da hallaka farar hula da dama a kauyen Kukawa-Gari, da ke karamar hukumar Gujba a jihar Yobe.

Rundunar ta ce jiragen yaki na soji sun yi ta shawagi a yankin kuma babu wani bayani game da kai hari a yankin.

Kazalika rundunar sojin ta ce sojojin ta na samun galaba a kan mayakan kungiyar Boko Haram wadanda aka tarwatsa wuraren da suke boye.

Rundunar sojin ta ce dakarun ta sun yi nasarar cafke wasu shugabannin Boko Haram biyu a garin Geidam na jihar Yoben.

Kakakin rundunar sojin kasa ta Najeriya, Kanar Sani Usman Kukah Sheka, ya shaida wa BBC cewa a halin yanzu daukacin hedikwatar sojin kasar na garin Maiduguri, inda suke kai dauki a duk wasu wurare da aka samu rahotannin kai hari daga kungiyar Boko Haram.

Tun da fari dai rahotannin da aka samu a ranar Talata sun ce mutane a kalla 60 ne suka rasu ta hanyar ko dai nutsewa a ruwa, ko harbin bindiga a lokacin da suke kokarin gujewa harin 'yan Boko Haram a jihar Yobe da ke arewacin Nigeria.

Rahotannin sun kuma ce lamarin ya faru ne a ranar Alhamis da ta gabata amma sai yanzu ake samun bayanai kan batun.