Ganyen 'sweetgrass' na maganin sauro

Image caption Asalin kabilun Amurka da ke garin Montana da Alberta, suna kitsa ganyen kuma su rataya shi a gidajen su.

Wasu masana kimiyya sun gano sinadaran da ke maganin sauro a wani ganye da ake cewa "sweetgrass", ganyen da wasu 'yan kasar Amurka ke amfani da shi wwajen korar kwari.

Gwaje-gwajen da aka yi ya nuna sinadarai biyu cikin ganen na 'sweetgrass' ya kori sauro daga samfurorin jini na karya, da aka ajiye domin gwaji, kamar yadda 'Deet' da aka fi sani da korar sauro ya ke yi.

Ana bukatar a kara gwaji, domin sanin tsawon lokacin da suke korar sauron.

Masu bincike sun ce magungunan gargajiya sun fi inganci wurin maganin sauro, inda Dr. Charles Cantrell wani ma'aikacin sashen Noma a kasar Amurka, mai bincike akan sinadarai ya ce, "wannan shi ne ganye na hudu da muka yi wa irin wannan bincike, kuma abin farin cikin shi ne yana fitar da wani sinadari mai kamshi, mara illa kuma mai maganin sauro, wanda ake cewa 'coumarin' ."

Dr Cantrell ya kara yin bayani a wani taron Kungiyar masu bincike kan Sinadarai a Amurka a garin Boston, inda ya bayyana wa manema labarai cewar kamfanin mai na 'Avon' yana amfani da sinadarin 'coumarin' a man shafawarsa mai suna 'skin so soft', kuma mutane sun gano cewar man yana maganin sauro.

"Ba a rubuta cewar yana maganin sauro ba, amma mutane da dama sun san cewa yana yi." In ji Dr. Cantrell.

Juriyar Sindarin

Hakkin mallakar hoto thinkstock
Image caption ASkwai bukatar samun sauyi a magungunan sauro da ake amfani da su yanzu, irin su 'Deet'.

Dr Cantrell ya fitar da wadannan sinadarai ta hanyar sirace, inda ya raba maikon ganyen da iska mai guba, sannan kuma ya tsaftace su ya kuma kasa su gida 12.

Wadannan kaso 12 ne aka yi gwajin sauron da su.

Bayan an gama gwaje-gwajen, Dr. Cantrell ya bayyana cewar, an gano sinadaran 'coumarin' da 'phytol' sune wadanda suka fi shahara.

Ya ce "Cikin mintuna uku, an gano cewar sindaran suna maganin sauro kamar yadda 'Deet' ya ke magani shi ma."

Yanzu dai likitan ya ce saura a gwada ne tsakanin mutane, domin a san jurewar sa, tunda yanzu an gano zai kai mintuna uku, amma zai iya jurewa har sa'o'i uku?

Wadannan tambayoyi zasu samu amsa nan da shekara daya ko biyu.