Yunkurin sa takunkumi a Sudan ta Kudu

Hakkin mallakar hoto
Image caption Jagoran 'yan tawaye Riek Machar, ya zargi gwamnatin Sudan da ci gaba da kai hare haren soji

Amurka ta ce ta fara yunkurin tattaunawa a Majalisar Dinkin Duniya kan batun sanya takunkumi ga duk wasu da ke yin zagon kasa ga batun samar da zaman lafiya a Sudan ta Kudu.

Amurkar ta kuma bayyana takaicinta kan kin sanya hannu a yarjejeniyar da aka cimma da shugaba Salva Kiir ya yi.

Gwamnatin Amurkar ta ce za a fara tattauna batun takunkumin da zarar Mista Kiir ya ki sanya hannu a karshen kwanaki 15 na sake yin nazari da gwamnatin Sudan ta Kudu ta bukata.

Shi dai jagoran 'yan tawaye Riek Machar, ya zargi gwamnatin Sudan din da ci gaba da kai hare-haren soji, yana mai cewa gwamnatin ta zabi yaki fiye da zaman lafiya.