Harin bam ya jikkata mutane 22 a Masar

Image caption Harin bam a Masar

Akalla mutane 22 ne suka jikkata da suka hada da 'yan sanda guda 6 a birnin Alkahira da ke Misra sakamakon fashewar wani bomb a arewacin kasar.

An dai ce an tayar da bomb din ne da safiyar ranar Alhamis da na'urar sarrafa abubuwa daga nesa ta 'remote control' a wani wurin da jami'an tsaron suke.

Wannan dai shi ne hari na baya-baya a cikin jerin hare-haren da aka kai kan jami'an tsaro a kasar.

tashin bomb din dai ya ragargaza tituna sannan kuma ya ruguza ginin da bun ya afku a ciki.

Mazauna yankin sun ce tashin bomb ya warwatsa glass din tagogogin ginin zuwa kan tituna.

Wannan harin dai na zuwa ne 'yan kwanaki bayan da shugaban kasar, Abdul-FATAH Al-sisi ya rattaba hannu akan dokar dakile ayyukan masu rajin yin jihadi.

Kawo yanzu ba bu wani wanda ya dauki alhakin kai harin.