Firayim ministan Girka ya yi murabus

Firayim ministan Girka Alexius Tsipras Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Firayim ministan Girka Alexius Tsipras

A wani jawabin da ya yi wadda aka watsa kai tsaye a gidan talabijin din kasar, ya ce gwamnatinsa ta yi aiki tukuru wajen cimma yarjejeniyar ceto tattalin arzikin kasar

Yace yanzu lokaci ne da 'yan kasar za su yanke hukunci.

Firayim ministan ya fuskanci zazzafar adawa a cikin jam'iyyarsa ta Syriza bayan da ya amince da daukar tsauraran matakan tsuke bakin aljihu domin samun dala biliyan casa'in da biyar cikin shekaru uku.

Rahotanni sun ambato jami'an gwamnatin na cewa za'a gudanar da zaben nan da wata daya.