Kwale-kwale ya nutse da mutane tara a Nijar

Image caption Ambaliyar ruwa ce ta janyo kifewar kwale-kwalen

Mutane tara sun rasu yayin da kwale-kwalen da suka shiga domin ketara wani makeken tafki ya nutse da su a jamhuriyar Nijar.

Mutanen sun fito ne daga kauyukansu domin zuwa gona.

Hukumomin yankin Walam da ke jihar Tilabery inda hadarin ya faru sun tabbatar da aukuwar hadarin.

Bayanai sun ce daga cikin wadanda suka tsira hadda wata mata da jariri mai watanni takwas a duniya.

Rahotanni sun nuna cewar hadarin ya auku ne sakamakon ambaliyar ruwa bayan da aka shafe sa'o'i ana ruwan sama kamar da bakin kwarya sannan kuma rafuka sun cika.