An fara binciken lafiyar jiragen saman Nigeria

Image caption An sha nuna bukatar a binciki lafiyar jiragen sama

Hukumar kula da lafiyar jiragen sama a Naijeriya wato NCAA, ta fara gudanar da binciken kamfanonin jiragen sama a kasar.

Binciken ya zo wa da yawa daga kamfanoni jiragen saman a ba zata.

Sai dai hukumar NCAA ta ce matakin gudanar da binciken ba wani abu ne da ya saba wa tsarin gudanar da bincike jiragen sama na kasa da kasa ba ne .

Darakta Janar na hukumar Captain Mukhtar Usman, ya ce abinda hukumar take a yanzu zai dawo da martabar makomar harkokin jiragen sama a Najeriya.

Ya kara da cewa "Bai kamata masu kamfanin jiragen sama a kasar su dauki al'amarin tamkar bita da kulli ba."

Tun a baya dai, al'ummar Najeriya sun sha nuna bukatar a binciki lafiyar jiragen sama na kasar, wanda mutane ke cewa hakan shi zai kara kwantar da hankulan masu hawa.