Samsung ya kaddamar da wayar da za a iya siyayya da ita

Hakkin mallakar hoto The Press Association
Image caption Wayar Samsung pay

Kamfanin Samsung ya kaddamar da sabuwar wayarsa wacce za a iya amfani da ita wajen yin siyayya a kantuna wato Samsung Pay a Koriya ta kudu.

Samsung ya bi sahun abokin gogayyarsa na Apple wajen bullo da wannan tsari.

Kamfanin ya ce zai iya samun kasuwa saboda fasahar da yake amfani da ita tafi aiki akan ta Apple a wurare daban-daban na cinikayya, dan haka nasu tsarin zai fi kasuwa akan na Apple.

A zahiri ba a tabbatar da cewa ko siyan kayayyaki ta hanyar amfani da wayar zai fi karbuwa a wajen jama'a ba, musamman idan ana maganar mutanen da suke tafiya da zamani.

Wannan tsari na amfani da wayar wajen siyayya a yanzu an takaita shi ne a kasar da cibiyar kamfanin take wato Koriya ta kudu.

Amma za a fadada tsarin zuwa Amurka a ranar 28 ga watan gobe, kazalika kamfanin ya ce kasashen Birtaniya da Spaniya da kuma China suma za su ci gajiyar wannan sabon tsari.

Hakan dai ya nuna cewa nasu tsarin ya dara na Apple, domin kuwa a kasashen Amurka da Birtaniya kawai ake iya amfani da tsarin na siyayya da waya maimakon ayi amfani da kati.

Za dai a iya amfani da wannan tsarin ne kawai da sabbin wayoyin kamfanin na komai da ruwanka samfurin Android.