MDD na son Senegal ta halatta zubar da ciki

Hakkin mallakar hoto thinkstock
Image caption MDD na son Senegal ta halatta zubar da ciki

Majalisar Dinkin Duniya na son kasar Senegal ta halatta tsarin zubar da ciki, ga matan da suka samu juna biyu sanadiyar yi musu fyade ko idan lafiyar mai juna biyu na cikin hadari.

A shekarar 2004 kasar ta Senegal ta rattaba hannu a kan yarjejeniyar Maputo a kan 'yancin mata a nahiyar Afrika.

Sai dai bayan shekaru 11 da yin haka, dokokin kasar sun amince a zubar da ciki ne kawai idan lafiyar mahaifiyar na cikin hadari.

An dai yi kiyasin cewa yawan cikin da ake zubarwa a kowace shekara a kasar ta Senegal ya kai 51,000.