Kun san illar yin aiki na tsawon sa'o'i a yini ?

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

Wani bincike da aka yi a kan mutane sama da rabin miliyan kuma aka wallafa a mujallar 'Lancet Medical Journal', ya nuna cewar mutanen da suke aiki na tsawon sa'o'i za su iya kamuwa da cutar mutuwar barin jiki.

Binciken ya kuma nuna cewar yiwuwar mutuwar barin jiki ga mutane masu aiki na tsawon lokaci ya karu fiye da, na masu aiki tsakanin karfe tara na safe zuwa karfe biyar na yamma.

Ba a tabbatar da alakar ba, amma kuma ka'idojin sun hada da aiki mai wahala da kuma illarsa a kan rayuwar mutum.

Masana sun ce ya kamata mutane wadanda suke aiki na tsawon sa'o'i su rika duba yanayin jininsu.

Binciken ya nuna cewa da aka kwatanta wadanda ke aikin sa'o'i 35-40 a mako, da wadanda ake aikin sa'o'i 48, za a ga cewar wadanda suke aikin sa'o'i sun fi fuskantar hadarin kamuwa da mutuwar barin jikin.

Dr Mika Kivimaki, maikacin jami'ar kwalejin da ke London ya ce, mutane wadanda suke aikin sa'o'i 35 zuwa sa'o'i 40, kadan ne a cikin mutane biyar masu mutuwar barin jiki a cikin ma'aikata 1,000 a cikin shekaru 10.

Kuma wannan adadin ya karu zuwa mutane shida masu mutuwar barin jiki a ma'aikata 1,000 cikin shekaru 10 a wadanda suke aiki na tsawon sa'o'i 55 ko sama da haka.

'Daskarewar jinin kwakwalwa'

Dr Kivimaki ya ce har yanzu masu bincike suna mataki na farko wajen gano abin da ke faruwa.

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

Wasu ra'ayoyin sun hada da gajiya saboda da karin yawan sa'o'i na yin aiki ko kuma zama wuri daya na tsawon lokaci ba shi da kyau ga lafiyar mutum.

Kuma hakan zai iya kara hadarin kamuwa da mutuwar barin jiki.

Duk da haka, zai iya zama wata alama da ke nuna rashin kyawun lafiya ga wadanda suke shafe tsawon sa'o'i a wurin aiki ba su da lokacin dafa abinci mai gina jiki ko motsa jikinsu.

Dr Kivimaki ya shaida wa BBC a intanet cewa "Ya kamata mutane su lura da cewar ya kamata su tafiyar da lafiyayyar rayuwa kuma su tabbatar bai karu ba."

Dr Shamim Quadir na kungiyar kula da mutuwar barin jiki ya yi sharhi da cewa " Yin aiki na tsawon sa'o'i zai iya kunsar zama a wuri daya na tsawon saoi, kuma hakan na saka gajiya kuma ya jawo karancin lokacin da mutun zai kula da kansa."

" Muna bayar da shawarar a yawaita duba hawan jini, idan har ka damu da yuwuwar kamuwa da cutar mutuwar barin jiki to ka nemi likita domin a yi gwaji," in ji Qaudir

Dr Tim Chico, likitan da ke kula da zuciya da ke jami'ar Sheffield da ke Ingila ya ce: " Mafi yawancin mu za mu iya rage yawan lokacin da muke shafewa a zaune a wuraren aiki, mu kara yawan motsa jiki kuma mu ci abinci mai kyau a yayin da muke aiki kuma hakan zai fi muhimmanci a kan yawan lokutan da muke yi a wajen aiki."