An fi fuskantar zafi a watan Yulin bana a duniya

Gwamnatin Amurka ta ce an fi fuskantar zafi a watan Yuli bana a duniya tunda aka fara adana bayanai a kan yanayi.

An samu karuwar zafi mai tsanani a doron kasa da tekuna yayin da wasu larduna su ma suka fuskanci zafi mai tsanani.

Hukumar kula da bincike kan teku da yanayi na kasa ta yi kiyasin cewar shekarar 2015 za ta kasance shekarar da tafi ko wacce zafi tun bayan da aka fara ajiye bayanai a kan yanayi a shekarar 1880.

Hukumar ta ce alkaluma na baya bayan nan sun tabbatar da batun da ake yi na sauyin yanayi, kodayake ta wani bangaren za a iya cewa karuwar zafin yanayi cewa sauyin yanayin da tekun Pacific ke haifarwa shi ke sa wa yanayin zafi na karuwa.