'Yemen za ta fuskanci karancin abinci'

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mai yiwuwa Yemen za ta fuskanci matsalar karancin abinci

Hukumar abinci ta Majalisar Dinkin Duniya, WFP, ta yi gargadin cewa bayan watannin da aka shafe ana gwabza fada a Yemen, kasar na gab da fadawa cikin matsalar matsanacin karancin abinci.

Hukumar ta bayyana haka ne bayan da aka kai hari ta sama a kan tashar jiragen ruwa ta Hodeida a daren Talatar da ta gabata.

Babban jami'in hukumar da ke kula da ayyukan jin kai a Majalisar Dinkin Duniya, Stephen O' Brien, ya soki lamirin dakarun hadakar da Saudiyya ke jagoranta bisa kai harin, yana mai cewa wannan mataki ya sabawa dokokin kare hakkin dan-Adam na duniya.

Mista O' Brien ya ce akwai jirgin hukumar ta WFP a tashar dauke da kayan agaji lokacin da aka kai harin.

Ya ce, "Na damu kwarai kasancewar barnar da aka yi a tashar jiragen ruwan Hodeoda zai iya yin mummunan tasiri a kan kasar gaba daya zai kuma kara yawan mutanen da ke fuskantar karancin abinci."