'An ci zarafin 'yan adawa a Burundi'

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Duk da mummunar zanga-zangar da aka yi sai da Shugaba Nkurunziza ya sake tsayawa takara.

Kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty International ta yi zargin cewa jami'an tsaro sun ci zarafin mutanen da ke goyon bayan 'yan adawa a lokacin zaben da ya gabata.

Kungiyar ta ce an rika dukan mutanen da karafuna, sannan aka rika watsa musu ruwan guba na acid.

Amnesty ta ce shaidun da ta tattaro sun nuna mata cewa 'yan sanda da jami'an leken asiri na kasar sun azabtar da mutane bayan sun tsare su ba bisa ka'ida ba, kana suka tilasta musu amincewa da laifin da ba su aikata ba.

Kungiyar Amnesty ta ce ba a bai wa lauyoyi damar kare mutanen a kotu ba.

'Yan adawa dai sun soki matakin da Shugaba Pierre Nkurunziza ya dauka na sake neman yin shugabancin kasar a karo na uku, suna masu cewa ya sabawa kundin tsarin mulkin kasar, kuma lamarin ya yi sanadiyar yin mummunar zanga-zanga.