Mutanen Bauchi sun koka kan ambaliyar ruwa

Image caption Ambaliyar ruwa ta shafi kananan hukumomi 10 na jihar Bauchi

Rahotanni daga Jihar Bauchi a Najeriya na cewa dumbin wadanda bala'in ambaliyar ruwa ya shafa a sassa daban-daban na jihar, na kokawa kan abin da suka kira 'mawuyacin hali' da suke ciki, ta fuskar karancin abinci da muhalli.

Wadanda abin ya shafa sun ce har yanzu ba su samu wani taimako daga mahukunta ba.

Matsalar dai ta shafi kananan hukumomi goma ne daga cikin kananan hukumomi 20 na jihar, da suka hada da Dambam da Jama'are da Kirfi da Alkaleri da Dass da Tafawa Balewa da Bogoro da Toro da Darazo da kuma Misau.

Daraktan tsare-tsare da kididdiga ta hukumar agaji ta jiha wato, Malam Shehu Abu Ningi, ya ce duk da cewa an kai wa wasu wuraren kayan agaji, har yanzu suna kan aikin tantance hakikannin yawan hasarar da ambaliyar ta haifar.

Ya kara da cewa "sai mun kammala tantancewar sannan za a kai kayan agaji, kuma a hakikanin gaskiya har zuwa yanzu ba a tanadi sansani domin wadanda bala'in ya shafa ba."

Ambaliyar ruwan da ta shafi jihar a kwanakin baya-bayan nan dai ta haifar da gagarumar barna ga gidaje da gonaki, gami da hasarar rayukan bil-Adama.