Ayyukan masanantu sun ragu a China

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wata masananta a China

Ayyukan masanantu a China sun ragu sosai ta yadda basu taba kaiwa a cikin shekaru shida da suka gabata a cikin wannan wata na Agusta, inda haka ke kara nuna wata alamar na koma baya da ga kasa ta biyu mafi karfin tattalin arziki a duniya.

Wannan ya nuna cewar ayyukan masanantu sun kara raguwa a watannin da suka gabata.

An rufe kasuwar hannun jari ta shanghai inda darajar hannun jarin ta ya yi kasa da kashi hudu bisa dari kuma alkaluman baya bayan nan sun sa ana ganin hakan zai saka kasuwannin hannun jarin kasashen Turai da na Asiya suma za su yi ksa.

Masu sharhi sun bayyana fargabar cewar tattalin arzikin China yayi kasa sosai a kan alkaluman da hukuma ta fitar na kashi bakwai bisa dari shekara.