Shugaban Rundunar 'Yan sandan Najeriya
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Matsalar aikin dan sanda

Daga rashin isassun kayan aiki, zuwa rashin biyan 'yan sanda hakkinsu da kuma zargin take hakkin bil'dama, aikin dan sanda a Najeriya na cike da matsalolin da ke bukatar magani cikin gaggawa, ganin irin kalubalen tsaron da kasar ke fama da su.

A baya dai an sha kafa kwamitoci, kuma an sha yin tarukan bita, inda aka bada shawarwari a kan yadda za a shawo kan matsalolin aikin.

Menene matsalolin da ake fuskanta a aikin kuma ta yaya za a inganta shi?