Kotu ta daure 'yan Luwadi a Senegal

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Abin kunya ne Luwadi a Afirka

An sanar da kotun cewa mahaifiyar daya daga cikin wadanda ake zargi ce ta baiyanawa 'yan sanda cewa dan ta dan Luwadi ne.

Wasu sun ce an kama ragowar ne suna aikata Luwadi yayin da yan sanda suka kai musu samame.

Kasashen yammacin Afirka sun haramta Luwadi inda laifin kan dauki hukuncin daurin shekaru biyar a gidan yari da kuma tara ta kimanin dala 2,500.

Har yanzu dai batun Luwadi babban abin kunya ne a Senegal inda kashi 95 cikin dari na jamaarta musulmi ne.