An sa tukwicin $1,000 kan masu fyade a Saliyo

Image caption Al'amarin ya girgiza 'yan kasar ta SAliyo

Gwamnatin Saliyo ta sanya tukuwicin dala 1,000 ga duk wanda ya taimaka wajen gano wasu gungun mutane da suka yi wa wata yarinya fyade har ta mutu.

An gano gawar Hannah Bockarie a makon da ya gabata a wajen wani teku da ke Freetown babban birnin kasar.

A ranar Alhamis da daddare ne aka yi kwanan addu'a ga mammaciyar.

Ministan harkokin mata na Saliyo Moijueh Kaikai, ya fashe da kuka lokacin da ake gabatar da addu'o'in, ya kuma yi alkawarin gabatar da matsalar a gaban majalisar zartarwa ta kasar.

Wakilin BBC a Saliyo ya ce mutane da dama sun girgiza da ganin hotunan gawarta a kafofin sadarwa na zamani.

An kuma kaddamar da wani kamfe a kafofin sada zumuntar inda har aka kirkiri maudu'i mai taken #iamhannah, wato "ni ce Hannah".