An yankewa Mohammed Badie daurin rai-da-rai

Wasu mambobin jam'iyyar 'yan uwa musulmi Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Gwamnatin Masar ta cafke dubban mambobin jam'iyyar 'yan uwa musulmi.

Wata kotu a kasar Masar ta yankewa jagoran jam'iyyar 'yan uwa musulmi Muhammad Badie hukuncin daurin rai-da-rai.

An yanke masa hukuncin tare da wasu masu fada aji na jam'iyyar 'yan uwa musulmi, bisa zargi da hannu a harin da aka kai caji ofis din 'yan sanda da ke Port Said a shekarar 2013.

Ana tuhumar Mr Badie da manyan laifuka da dama, inda wata kotun ta daban a Masar ta yanke masa hukuncin kisa a watan Afirilun da ya wuce.

Kuma ya na daga cikin dubban mambobin jam'iyyar 'yan uwa musulmi da aka garkame a gidan kaso, da tuhumar taimakawa gwagwarmayar da ta tabbatar da shugaba Mohammed Morsi darewa karagar mulkin kasar, kafin daga baya sojoji su yi juyin mulkin da ya hambarar da gwamnatinsa.