An kashe mutane 10 a Jamhuriyar tsakiyar Afrika

Hakkin mallakar hoto
Image caption Francois Bozize

A kalla mutane 10 ne suka rasa rayukansu a yayin wata gwabzawa tsakanin musulmai da mabiya addinin kirista a jamhuriyar tsakiyar Afrika.

Rahotanni sun ce fadan ya samo asali ne bayan da mabiya addinin kirista 'yan kungiyar Anti balaka suka kashe wani yaro musulmi a tsakiyar yankin Bambari.

Hakan ne ya janyo ramuwar gayya daga musulman.

Juyin mulkin da akayi a Jamhuriyar ta tsakiyar Afrika a shekarar 2013 ya haifar da gagarumin rikici tsakanin Musulmai da sojojin sa kai na bangaren Kirista lamarin da ya janyo mutuwar dubban mutane.