Likitoci a Ghana sun janye yajin aiki

Asibiti a kasar Ghana
Image caption Likitocin na korafin gwamnati ta gagara biya musu bukarun su.

Likitoci a kasar Ghana sun janye yajin aikin makwanni 3 da suka tafi, bisa korafin rashin kyawun wurin aiki da karin albashi da alawus-alawus.

Mako guda kenan da tafiya yajin aikin, wanda ya janyo aka rufe babban asibitin kasar na tsahon wannan lokaci.

Shugaban kungiyar likitocin Ghana ya ce gwamnati ta gagara cika musu alkawurran da ta dauka dan haka ne ma suka tsunduma yajin aikin.

Sai dai yace a yanzu daukacin mambobin su za su koma baki aiki, ya yin da za a ci gaba da tattaunawa kan bukatun nasu.

A makon da ya wuce hatta sashen kula da marasa lafiya na gaggawa wato Emergency Unit sai da likitocin suka janye ayyukansu.

Inda masu sharhi kan al'amura ke ganin yajin aikin, masu karamin karfi wadanda ba za su iya zuwa asibitoci masu zaman kansu ba zai sha fa.