Ana aikin ceton 'yan ci-rani daga teku

'yan gudun hijira Hakkin mallakar hoto AFP

Sojin ruwan Italiya sun ce sun sami nasarar tsara aikin ceto 'yan gudun hijira fiye da dubu biyu a kan Tekun Libya.

An kaddamar da aikin ceton ne bayan da jiragen ruwa fiye da ashirin makare da mutane suka aika da sakon gaggawa na neman ceto.

Aikin ceton ya hada da sojin ruwa da dama da kuma jiragen ruwa.

Daga cikin wadanda aka ceto sun hada da mutane fiye da dari tara a cikin jiragen ruwa guda biyu, wadanda suka fuskanci hadarin nutsewa a kan Tekun na Libya.

Wannan dai shi ne gagarumin aikin ceto mafi girma da aka gudanar a rana guda a kan tekun.

Yayin da aka fara shiga duhun dare aikin ceton na ci gaba da gudana, sai dai babu tabbas a kan ko mutane nawa ne da mai yiwuwa har yanzu suke cikin hadari.