Tsugune ba ta kare ba a kasashen Koriya

Shugabar Koriya ta arewa Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kasashen biyu sun dade su na nunawa juna yatsa.

Koriya ta arewa da Koriya ta kudu sun shiga rana ta biyu ta tattaunawa da nufin sassauta cacar baki akan iyakokinsu.

Duk da tattaunawar da ke gudana sojojin Koriya ta kudu sun ce sun gano kai komon sojoji da ba'a saba gani ba da kuma jiragen ruwa na karkashin teku a Koriya ta arewa.

Wanda ke nuna alamar cewa Pyongyang tana jibge makamai da dakaru na maiyiwuwar shirin kai hari.

Wani jami'in ma'aikatar tsaro a Seoul yace Koriya ta arewa ta rubanya yawan sojojinta na artilary tun bayan fara tattaunawar kolin a jiya.