An ceto 'yanci rani dubu uku

Image caption 'Yanci rani

An ceto kusan 'yanci rani dubu 3 daga cikin wadanda suke cikin jiragen ruwa da suka nemi taimakon gaggawa a tekun Libya.

Masu tsaron tekun sun gudanar da aikin ceton ne bayan da suka samu sakon neman agaji daga jiragen ruwa fiye da ashirin makare da mutane a tekun.

Daga cikin wadanda aka ceto sun hada da mutane fiye da dari tara a cikin jiragen ruwa guda biyu, wadanda suka fuskanci hadarin nutsewa a kan Tekun na Libya.

Wannan dai shi ne gagarumin aikin ceto mafi girma da aka gudanar a rana guda a kan tekun.

Babu dai rahoton samun rauni ko rasa rai a cikin 'yanci ranin.