Faransa ta karrama mutane 4

Shugaban Faransa, Francois Hollande ya karrama mutane huɗu da lambar yabo mafi daraja a ƙasar saboda bajintar da suka nuna wajen katse hanzarin wani mai shirin kai harin ta'addanci.

Lamarin dai ya auku ne a jirgin ƙasa ranar Juma'a.

Sojan Amurka Spencer Stone, wanda ya samu raunuka, a lokacin da ya fuskanci ɗan bindigar, da wasu Amurkawan biyu, da kuma ɗan Birtaniya guda ne aka karrama.

An yaba wa jaruntar da suka nuna.

Shugaba Hollande ya ce, ba dan jaruntar da mutanen hudu suka nuna ba da dan bindigar ya yi ta'adi.