An karawa malaman makarantun Kenya albashi

Hakkin mallakar hoto others
Image caption Malaman sun ce albashin da ake ba su bai ishe su ba.

Kotun kolin Kenya ta umarci gwamnatin kasar ta karawa malaman makarantu albashi zuwa kashi sittin ciki dari na kudin da ake ba su.

Ita dai gwamnatin ta sha cewa ba za ta iya biyan malaman kusan 200,000 karin albashi ba.

Sai dai bayan malaman sun gurfanar da gwamnati a gaban kotun, sun yi nasarar samun karin albashin.

Malaman sun yi barazanar tafiya yajin aiki idan ba a kara musu albashin ba.

Sun ce albashin da ake ba su ba ya isar su, domin kuwa wasun su suna daukar abin da bai wuce $100 a wata ba.