Ko me ke janyo shanyewar bangaren jiki?

Hakkin mallakar hoto Thinkstock
Image caption Aiki na tsawon sa'oi kan janyo shanyewar bangaren jiki wato stroke a Turance.

Masu bincike a jami'ar London sun ce aiki na tsawon sa'oi ga alamu na da alaka da karuwar hatsarin kamuwa da cutar nan ta shanyewar bangaren jiki wato stroke a Turance.

Masu binciken sun yin amfani da bayanan da suka samu daga dubban ma'aikata a nahiyar Turai da Australia da kuma Amurka.

Sun ce ma'aikatan da ke aikin fiye da sa'oi hamsin da biyar a mako na fuskantar hatsarin shanyewar bangaren jikin su fiye da wadanda suke aikin sa'o'i talatin da biyar zuwa arba'in.

Sun kuma ce dole ne mutanen da ke aikin sa'oi da yawa su maida hankali wajen irin abincin da suke ci, da kuma awon jinin su.