An bude hanya tsakanin Adamawa da Taraba

Hakkin mallakar hoto Nigeria Police website
Image caption Solomon Arase, shugaban 'yan sandan Nigeria

Direbobin manyan motoci da suka tsare babban haryar da ta hada jihohin Adamawa da Taraba don nuna fushinsu game da kisan da aka yi wa wani direba dan uwansu yanzu sun janye datsewar da suka yi wa hanyar.

Direbobin sun janye ne bayan da suka sasanta da jamian tsaro da kuma gwamnatin jihar Tarba.

Tuni dai rahotanni suke cewa zirga zirgar ababen hawa ta sake kankama a wannan babban titin.

Direbobin sun ce sun gaji da kashe musu 'yan uwa da suke zargin jami'an tsaro na yi idan sun ki ba su na-goro.

Ƙungiyar direbobin ta ce an kashe mata aƙalla direbobi uku, tare da jikkata wasu da dama sakamakon gardamar da take kaure tsakanin mambobinta da jami'an tsaro a kan na-goro a duk lokacin da suka yi dakon kaya.

Direbobin sun yi zargin cewa jami'an tsaro suna karbar kudi da suka kayyade daga kowacce motar daukar kaya.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sanda ta jihar Taraba ya ce, kwamishinan 'yan sanda ya je wurin da lamarin ya faru.