Yara goma sun mutu a Afghanistan

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption An samu fashewar iskar gas a garin Herat, inda ya yi sanadiyyar mutuwar yara goma a sansanin 'yan gudun hijra.

An samu fashewar wani abu a wata tashar iskar gas a garin Herat da ke yammacin kasar Afghanistan, inda ya yi sanadiyyar mutuwar wasu yara su goma da wani babba wadanda ke zaune a wani sansanin 'yan gudun hijra.

Wani kakakin asibiti ya ce fashewar abun ta kuma raunata mutane 18.

An kewaye shafukan sada zumunta da hotunan gobarar da ta kai har sama.

Amma ba a tabbatar da ko lamarin ya faru ne sakamakon hadari ko kuma hari ne na ta'addanci ba.