Bankuna sun rage kudin ruwa a China

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Farashin hannun jari ya fadi kasa warwas a China

Bankuna a kasar China sun rage kudin ruwa a wani kokari na dakatar da rugujewar da farashi a kasuwar hada-hadar hannayen jari ke yi.

Hannun jari a kasuwar Shanghai ya yi kasa da kashi bakwai cikin dari, bayan faduwarsa a ranar Litinin da kashi takwas da rabi cikin dari.

Wannan dai shi ne karo da biyar da Chinan ke rage kudin ruwanta tun daga watan Nuwanbar bara.

Kasuwannin hada-hadar hannayen jari a Turai da Australia su ma sunbi sahu.

Kiyasin da aka yi ya nuna irin hasarar biliyoyin daloli da aka yi a sanadiyyar faduwar farashin hannayen jari a duk fadin duniya ranar Litinin.