Zan shirya taro kan Boko Haram - Hollande

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaban Faransa, Francois Hollande ya ce a shirye ya ke ya dauki nauyin shirya taron kasashen duniya kan yaki da Boko Haram.

Shugaban Faransa, Francois Hollande, ya ce a shirye yake ya dauki nauyin shirya taron kasashen duniya kan yaki da Boko Haram.

Shugaban ya bayyana hakan ne a wani jawabi da ya yi wa jami'an diplomasiya kan tsaro a birnin Paris na kasarsa.

Hollande ya yi gargadin cewar Faransa tana fuskantar barazanar ta'addanci, saboda haka ya zama dole ta shirya wa duk wani hari da za a kawo mata.

Mr. Hollande ya bayyana haka ne kwanaki kadan bayan wasu fasinjoji sun dakile wani yunkurin kai hari da wani dan ta'adda ya yi yunkurin yi a wani jirgin kasa a Faransan.

Mr. Hollande ya kara da cewar yana so ya kafa wata kungiyar tuntuba ta kasa da kasa, wacce zata farfado da shirin samar da zaman lafiya a gabas ta tsakiya, kuma ta hada taron da zai tattauna a kan hanyoyin da za a bi wajen dakile kungiyar Boko Haram a Najeriya