An daure mai kutse a wayoyin salular Aviva

Hakkin mallakar hoto
Image caption Richard Neale ya amsa aikata laifin kutse a wayoyin salula don daukar fansa.

An yankewa wani mutum daurin watanni goma sha takwas a gidan fursuna bayan da aka same shi da laifin kutse a wayoyin salula guda dari tara na kamfanin Aviva mai harkar Inshora.

Richard Neale, mai shekaru arba'in ya amsa cewa ya aikata laifin kutse a wayoyin salular don daukar fansa bayan da ya samu sabani da abokan sa.

Shi dai mutumin ya taba rike mukamin direkta a kamfanin Esselar, wanda kamfanin Aviva ya ba kwangilar samar da tsaro a hanyoyin kamfanin na Internet.

Ya kuma amince cewa ya yi kutse a rumbun bayanai na Aviva a watan Mayun shekarar 2014 a daren da aka ba Esselar damar yin gwaji na aikin samar da tsaro ga kamfanin Aviva.