An rufe shafin Agora

Hakkin mallakar hoto THINKSTOCK

Kamfanin Dark Web ya ce shafinsa na internet watau Agora ya ce zai cigaba da kasancewa a rufe saboda ba zai iya tabbatar da tsaro ga masu amfani da shafin ba.

Kamfanin ya ce fargabar da wasu suka nuna akan cewa za'a iya sanin ainihin inda masu amfani da shafin suke na cikin dalilan da suka sa aka rufe shafin.

Shugabannin kamfanin sun ce shafin zai ci gaba da kasancewa a rufe har sai an bulo da wani mataki mai dorewa a kan yada zasu shawo kan matsalar.

A cewar Graham Cluley wanda kwarare ne kan harkar tsaro, lamarin ya nuna cewa masu amfani da shafin ba su da kwarin gwiwa cewar shafin zai iya tabbatar mu su da tsaro.

Mutane kan yi amfani da shafin na Agora wajen siyan tare kuma da sayar da miyagun kwayoyi.

Sai dai a watan daya gabata ne shafin ya sanar cewa ya hana sayar da bindigogi .