Miyagun kwayoyi: An kama ma'aikacin Arik a London

Hakkin mallakar hoto BOEING MEDIA
Image caption An kama ma'aikacin Arik da hodar Ibilis a London.

A daren Litinin ne jami'an tsaron kan iyakar Biritaniya suka kama wani ma'aikacin kamfanin jiragen sama na Arik Air, Chika Egwu Udensi, dauke da hodar ibilis mai nauyin kilo 20.

An kama Udensi ne a filin saukar jiragen sama na London Heathrow, bayan binciken da hukumar yaki da shan miyagun kwayoyi a Najeriya, watau NDLEA, ta yi a motarsa wadda ya ajiye a filin saukar jiragen sama na Murtala Muhammad da ke Lagos.

Wannan ba shi ne karo na farko da a ke kama ma'aikatan Arik da miyagun kwayoyi ba.

Shekaru biyu da suka gabata ma jami'an tsaron kan iyakar Biritaniya sun kama wasu ma'aikatan kamfanin su biyu.