Za a rinka goge muhimman bayanan mutum a shafin Ashley Madison

Hakkin mallakar hoto AP

An samu wasu karin matakai da za a dauka bayan satar bayanan da masu kutse a shafin sada zumunta na ma'aurata wato Ashley Madison suka yi.

An dai wallafa wani rahoto a shafin inda aka yanke shawarar cewa za a rinka goge duk wasu muhimman bayanin ma'abota shafin.

Sai dai kuma za a rinka barin wasu bayanai na masu amfani da shafin wadanda suka hadar da ranar haihuwa da kuma jinsin mutum a shafin.

Wannan dai zai bawa masu amfani da shafin damar saka ko kuma goge duk wani bayanin su saboda gudun masu kutse a shafin.

Sakamakon sakin bayanai da masu kutsen suka yi wadanda yawansu ya kai gigabytes 10 da suka sato a shafin na Ashley Madison a makon da ya gabata , yanzu an bayar da shawar cewa a rinka goge muhimman bayanan da mutum baya so a sani ko a gani.

Yawancin kwararru a bangaren tsaro ciki har da Brian Krebs sun yi amanna cewa bayanan na gaskiya ne.

Masu amfani da shafukan intanet zasu iya amfani da shafin na Ashley Madison ba tare da sun bi dokar tantance adireshin su na email ba.

Hakan dai na nufin za a iya kulla alaka da kowanne adireshi na email, saboda ba a bin diddigi.

To sai dai duk da wannan ikirari na masu kutsen, wani labari mai dadi ga masu amfani da shafin Ashley Madison shi ne lambobin sirrin su na shiga shafin har yanzu suna nan akan tsarin da ake dashi na yadda za ayi wahalar gane su.

Dangane da haka, ana ganin cewa abune da ya dace ga masu amfani da shafin Ashley Madison su canza lambobin su na sirri wato na bude shafin a wasu shafukan na daban.