Kotu ta sami James Holmes da laifi

James Holmes Hakkin mallakar hoto AP
Image caption James Holmes

Alkalin kotu a jihar Colorado a Amurka ya yanke hukuncin daurin rai da rai ga dan bindigar nan da ya kashe mutane 12 a wani gidan kallo shekaru uku da suka wuce.

James Holmes ya bude wuta ne lokacin da mutane su ke kallon fim din Batman da aka kadammar.

Wadanda suka tsira da kuma dangin mutanen da ya kashe sun rika shewa lokacin da aka fitar da Mr Holmes da ga cikin dakin kotun wanda aka sakawa ankwa.

A farkon watan da mu ke ciki masu sauraron karar su ka bayar da shawara a kan a yanke ma sa hukuncin daurin rai da rai bayan da suka kasa cimma matsaya akan hukuncin kisa.

Shi dai Holmes ya ce be aikata laifi ba saboda yana fama da ciwon tabin hankali.